Read❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) | Aysha_sona

Read ❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)  - IDNEWS24.com

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)

Authors: Aysha_sona

Genre: New Adult

Update: 03-10-2022

Status: Completed

Favorites / 4097669 Views
Read

Hassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos.

Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu.

"Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi nazari akai. Million d'ari, shekara biyar, and your brother is free. It's a contract." Waenan sune kalaman da kyakyawan billionaire Hassan Sooraj ya ra'da mun a kunne. Mutumin dake sa zuciyata hargitsi a duk sanda na daura idanuna akansa.

Ina so na kalli cikin kwayar idanunsa nace masa a'a amma taya zan fara? kanina yaci masa bashin naira million da'ya da'ya har d'ari. Bashin dana san har duniya ta na'de bazamu ta'ba iya biya ba saboda mu talakawa ne gaba da baya, ina zamu samu waenan makudan kudi mu biyashi?

Abunda yafi daure mun kai yafi bani takaici shine yanda zuciyata kulum take dalmiya cikin kogin sonsa, mutumin da bai daukeni a bakin komai ba sai abar wasarsa.

Sunana Hibba Abdullahi, shekarata ashirin da biyu a duniya, ni yar Biu ce, Babur gaba da bayanta, banida kowa banida komai sai kanina, gatanmun shine Allah. Shi kadaine zai iya fiddani daga tarkon wanan kyakyawan attajirin, mai dara daran idanu masu mugun firgitar mun da zuciya.

Wanan shine labarin mu.